Mutumin Kirki

Ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Allah Ya yi wa Alhaji Sani Muhammed Kangiwa, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kebbi rasuwa. Ya rasu ne a asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi bayan ya yi fama da rashin lafiya.

An haifi Marigayi Alhaji Sani Muhammed a garin Kangiwa a 1959, inda ya fara karatun addini da kuma na zamani. Ya riƙe mukaman siyasa da na gwanmati daban-daban da suka haɗa da shugabancin ƙaramar hukumar mulki ta Arewa, da daraktan yaɗa labarai a lokacin Kanal Salisu Tunde Bello yana gwamnan Kebbi a lokacin mulkin sojoji. Ya kuma riƙe mukamin sakataren jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.

Alhaji Sani Muhammed Kangiwa ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya 17, jikoki biyu da kuma mahaifiyarsa. An kuma yi jana’izarsa a garin Argungu ranar Litinin ɗin kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada. Sannan kuma Gwamna Saidu Dakingari, sakataren gwamnatin jihar Alhaji Nura Usman Kangiwa, Alhaji Mansur Shehu shugaban PDP na jihar Kebbi, kwamishinoni, daraktoci, ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya sun sami halartar jana’izar.

Alhaji Nura Usman Sakataren gwamnatin Jihar Kebbi wanda yake ɗan’uwan marigayin ne ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, ba ga iyalinsa kaɗai ba, ga duk faɗin jihar.



What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.