Glossary Page Original Source Text/Audio Information Page Additional Resources Page GLOSS Tutorial GLOSS Questionnaire
Lesson OverviewActivity 1Activity 2Activity 3Activity 4Activity 5
Illar Shan Barasa
Click for Teacher's Note Click for Instructions Click to Bookmark this Activity Reload Page - Clears Activity

Akwai Bukatar Rage Illar Shan Barasa      mashaya

Sabon rahoto na Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya yace barasa tana kashe mutane miliyan biyu da rabi kowace shekara a fadin duniya.
Wani sabon rahoton da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ƙaddamar ya ce ana buƙatar sabbin manufofi domin rage illar da shan barasa fiye da kima ke yi ga lafiyar jama'a. Yin amfani da barasa fiye da kima tana kashe mutane miliyan biyu da rabi kowace shekara, da janyo rashin lafiya da rauni ga wasu da dama, yayin da ta ke ƙara shafar matasa da masu shanta a ƙasashe masu tasowa.


Ana fassara "yin amfani da barasa fiye da kima" a zaman shan barasa ta yadda har zata shafi lafiyar wanda ya sha.Wannan rahoto da aka laƙabawa suna "The Global Status Report on Alcohol and Health" ya nazarci shaidar da ake da ita ta shan barasa, da illolinta ga lafiya da zamantakewar jama'a da kuma yadda huƙumomi ke takalar wannan batu a ƙasashe, da yankuna da kuma duniya baki ɗaya.


An gano cewa kusan kashi 4 cikin 100 na masu mutuwa a duniya kowace shekara, barasa ce take zamowa sanadinsu.Ƙasashe da dama ba su da shirye-shiryen hana mutane shan barasa fiye da kima. An ƙara yawan matakan daƙile tallar barasa da kuma tuƙi cikin maye a faɗin duniya, amma kuma babu wasu matakan zahiri na hana mutane shan barasar.


Nazarin bayanai daga shekarar 2001 zuwa 2005 ya nuna cewa yawan masu shan barasa bai ƙaru ba a ƙasashen nahiyar Amurka, da Turai da Gabashin tekun bahar Rum da kuma yankin yammacin tekun Pacifc. Amma an ga ƙaruwar yawan masu shan barasa sosai a nahiyar Afirka da yankin kudu maso gabashin Asiya a cikin wadannan shekarun biyar.


Amma kuma duk da cewa ana shan barasa a kowane lungu na duniya, a zahiri yawan mutanen da ba su shan ta sun fi masu sha yawa a duniya. Rahoton ya gano cewa a shekarar 2005, kusan rabin mazaje a faɗin duniya ba su sha barasa ba, yayin da kashi 67 cikin 100 na mata ba su sha barasar ba.Ƙasashen larabawa na Arewacin Afirka da kuma ƙasashen kudancin Asiya su ne suka fi gujewa shan barasa a duniya.


 
 
 
 
 
Check Answers
Copyright DLIFLC - 2011
Video Tutorial
close