Albishiri ga Afirka

Masauraro, albishirinku! Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta bada labarin cewa akwai yiwuwar kafin ƙarshen shekara ta dubu biyu da tara za a samu sabon allurar rigakafin Sanƙarau mara tsada.



A yayin da yanzu sauran kimanin watani uku kamin a fita daga lokacin da aka fi ganin annobar ciwon sanƙarau, bala’in annonba ta ƙasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kashe daruruwan mutane.



Ƙasashen Afirka da suka kama daga Senegal zuwa Ethiopia nan ne aka fi fama da matsalar annobar sankarau. Fiye da kashi biyu daga cikin uku na waɗanda ke kamuwa da ciwon a duk faɗin duniya, suna a wannan yankin. A bana kawai kimanin mutane ɗari uku da hamsin suka mutu a kasar Burkina Faso, a saboda sanƙarau.



Ƙwayar cutar wannan ciwo kan kai wa wani layi da ke kewaye da ƙwaƙwalwa da kuma ƙashin baya hari. Ko da an yi jinya ma, an bayyana cewa kimanin kashi goma daga cikin dari na waɗanda suka kamu da ciwon suka mutu.



An kuma fi ganin annobar sanƙarau ne a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuni.



Masanin sanƙarau a Ƙungiyar Lafiya ta Duniya Alexandro Costa ya ce allurar rigakafin cutar da ake yi amfani da shi a yanzu ba ya jinya yanda ya kamata domin kuwa:



“Kariya da yake bayarwa na shekaru biyu ne kurum. A saboda haka ana amfani da allura ne domin ƙayyada ɓullar annobar cutar, amma ba domin a yi wa mutane a sabili da su samu kariya na lokaci mai tsawo ba.”



Bugu da ƙari kuma Alexandro Costa ya ce allurar rigakafin da ake da shi yanzu ba ya kare ƙananan yara. Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta ƙirƙiro wani sabon allurar rigakafi da take fatar zai hana ɓullar annobar kafin ma ta fara: Ya ce: “Sabon allurar rigakafin zai bada kariya na a ƙalla shekaru goma.



Ya ce bisa bayanin da suka da su a yanzu, ana iya yi wa mutane allurar rigakafin hatta ma waɗanda ba a yi wa alluran ba za su ci moriya daga waɗanda aka yi wa allura domin allura zai takura ko kuma zai hana yaɗa kwayar cutar ta meningococcal.”



Wannan allurar rigakafi zai auna wani nau’i na sanƙarau da ake ce wa serotype da Turanci. Alexandro Costa ya ce wannan nau’i na sanƙarau ne ke da alhakin dukkan annobar sanƙarau da ake da su a nahiyar Afirka.



Ƙungyar Lafiya tana fatar sabon allurar rigakafin, wanda furashinsa ba zai wuce kimanin senti arba’in ba, zai taimaka wajen yi wa dukkan al’umma allurar rigakafi.



Alexandro Costa ya ce suna fatar kawar da sanƙarau nau’in serotype da wannan sabon allurar rigakafin. A farkon baɗi, idan Allah ya kai mu, ake sa ran fara rarraba wannan sabon allurar na rigakafin sanƙarau.





_TTEXT2ALT_
What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.