Tawagar ECOWAS a Ivory Coast

Jami'an yankin Afirka ta Yamma za su yi tattaki zuwa Ivory Coast domin shiga tsakanin gwamnati da sojojin ƙasar da ke yi mata tawaye.

A bayan sun gana yau litinin da shugaba Laurent Gbagbo, ministocin harkokin waje da na tsaro da ke cikin tawagar suna fatan shirya ganawa da sojoji masu tawaye da ke riƙe da birnen Bouake da wasu garuruwa na arewacin Ivory Coast.

An kafa wannan tawaga jiya lahadi, a lokacin wani taron gaggawar da aka yi na Ƙungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, a Accra, babban birnin Ghana.

Shugabannin ECOWAS sun yarda cewa ƙasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da Guinea-Bissau da kuma Togo su ne za su jagoranci wannan ƙoƙari na sasantawa.

Shugabanni a wurin taron na ECOWAS sun bayyana goyon baya ga shugaba Gbagbo, sun kuma ce za su tura runduna ta ƙasa da ƙasa ta sojoji dubu huɗu idan har ƙoƙarin sasanta tsakanin sassan ya ci tura.

Wannan ƙoƙarin sasantawa ya biyo bayan kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasashen wajen da sojojin Amurka da na Faransa suka yi jiya lahadi daga garin Korhogo na arewacin ƙasar, wanda ke hannun 'yan tawaye.

A hedkwatar MƊD, jakadan kasar Ivory Coast, Djessan Philippe Djangone-Bi, ya ce ƙasarsa tana son yakar 'yan tawayen da kanta. Ya ce rundunar sojan ƙasar tana sabunta makamanta, tana kuma bukatar karin makamai daga wasu ƙasashe domin murkushe wannan tawaye. Ya ce tuni har sojojin Faransa sun taimaka da kayan faɗa.

Har ila yau, Mr. Djangone-Bi ya yi zargin cewa 'yan tawayen suna samun agajin makamai daga wasu ƙasashe, amma bai faɗi ko su wane ne ba. Sai dai kuma ya ce 'yan tawayen sun samo asali ne daga Burkina Faso da Saliyo da kuma Liberiya. Babu wata kafar da ta gaskata wannan ikirari nasa.

A yau litinin, gwamnatin Ivory Coast ta ce ta ƙara tsawon wa'adin aiki da dokar hana yawon daren da ta kafa a faɗin ƙasar tun lokacin da aka fara wannan tawaye.



_TTEXT2ALT_
What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.