Glossary Page Original Source Text/Audio Information Page Additional Resources Page GLOSS Tutorial GLOSS Questionnaire
Lesson OverviewActivity 1Activity 2Activity 3Activity 4Activity 5
Ma'aikatanmu (Na Ɗaya)
Click for Teacher's Note Click for Instructions Click to Bookmark this Activity Reload Page - Clears Activity

Sunday DareSunday Dare

Sunday Dare shi ne shugaban Sashen Hausa. Kafin zuwansa nan Muryar Amurka a shekarar 2001, sanannen dan jarida ne a ciki da wajen Nijeriya. A shekarar 1998 Mr. Dare ya samu gurbin karo ilmin aikin jarida a Jami'ar New York. Ya kuma sake samun irin wannan gurbi zuwa Jami'ar Harvard dake Cambridge a Jihar Massachussetts a shekarar 2000.

Jummai Ali Maiduguri

Jummai Ali Maiduguri edita ce. Kuma ita ce ke gabatar da shirin nan na "Lafiya Uwar Jiki.” Jummai ta fara aiki a Muryar Amurka tun shekarar 1984. Kafin nan kuwa, Jummai ta yi shekaru da dama tana aikin jarida a Kaduna.

Aliyu Mustapha Sokoto

Aliyu Mustapha Sokoto, shi ma edita ne. Kuma shi ne jagoran shirye-shiryen nan na "Amsoshin Tambayoyinku" da "Labarin Wasanni.” Aliyu ya yi aiki a NTA Sokoto kafin ya taho nan Muryar Amurka a shekarar 1989. Aliyu ya jagoranci kungiyar nan ta "Zumunta" ta 'yan arewacin Nijeriya da ke Amurka na tsawon shekaru da yawa daga kafa ta.

Alhaji Kabiru Fagge

Alhaji Kabiru Fagge edita ne a Sashen Hausa, kuma shi ne ke jagorancin shirin "Ilmi Garkuwar Dan Adam" da "Sharhin Jaridun Amurka" a kowane mako. Alhaji Kabiru Fagge ya taho sashen Hausa na Muryar Amurka daga gidan telibijin na NTA Kano. Kafin nan kuwa ya yi aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian.

Grace Abdu

Grace Alheri Abdu ita ce ke gabatar da shirin “Domin Iyali.” Kafin ta kama aiki a Muryar Amurka mataimakiyar darekta ce a gidan rediyo da telibijin na jihar Plato (PRTVC).Tana da digiri a tauhidi da babban digiri a fannonin doka da diplomasiya, da kuma babban diploma a fannin aikin jarida.


 
 
 
 
 
 
Check Answers
Copyright DLIFLC - 2011
Video Tutorial
close