Wani Taro a Nijeriya

Mai Karanta Labari: A birnin Ikko kuwa sarakunan Fulanin jihohin kudancin Nijeriya ne suka yi wani taro domin tinkara matsalolin da ke addabar su da sana’arsu ta kiwo. Ladin Ibrahim Ayawa ya halarci wannan taro.

Ladan Ibrahim Ayawa: Sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammad Bambaɗo ya ce taron ya zama wajibi domin ganin cewa Fulani ba su shiga halin damuwa ba mussaman a game da wuraren da suke kiwon dabobinsu a duk faɗin jihohin kudancin Nijeriya.

Ya ce duk da yake suna fuskanta matsalar kabilanci da cinikin shanu duk inda suke a jihohin kudancin Nijeriya, to, amma, har kullum suna kira mutanensu lokaci-lokaci domin faɗakar da su muhimmancin zaman lafiya.

Alhaji Bambaɗo ya ce biyo bayan irin matsala da wasu Fulani suka shiga ne tsakanin su da masu masaukinsu a jihar Oyo ya sa suka gayyaci tsohon shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari domin ya shiga tsakani.

To, na tambayeshi ko mine ne dangantakarsu da gwamnatocin jihohin kudancin Nijeriya da har in sun samu matsala sai sun kira shugabanni daga arewa:

“Muna da kyakyawan dangantakar tsakanin mu da gwamnati. Su, muna tuntubensu suna shawara da mu. Mu ma muna shawara da su.”

Da kuma ya taɓo maganar rikicin da ke nema ya ɓullo kai a tsakanin Fulani a jihar Ogun. Sai sarki Bambaɗo ya ce wannan batu na ɗaya daga cikin manya-manyan batutuwan da suke tattaunawa a wannan zaman da suke yi a halin yanzu:

“Hauka ma ganin cewa Fulani sun yi nisa da ainahin muhallinsu.”

Hakan ya sa na tambayi Sardaunan Yamma Alhaji Salisu Bashanke ko cewa Fulani da ke kudancin Nijeriya za su amfana da ilimin zamani:

“Ku ma kun san cewa kowane lokaci kuna gani yanda muke taruruka kuma muke yin ƙoƙari cewa mu tabbatar cewar an gina ma Fulani makarantu a ƙasar nan, su ma su samu ilimi mai inganci kamar kowa.”

Shi ma sarkin Hausawa a Abeokuta, fadar gwamnatin Ogun Alhaji Hasan Hasan na cikin mahalarta wannan taron. Shi kuwa tambayarsa na yi, ko mi ya zo ya yi cikin taron Fulani:

“Makasudin halarta ta wannan taro shi ne: Ni dai, wannan al’amarin na Fulani a cikin jiha ta ya yi kyau, kuma ni ne ainahin sarkin sarakuna na jihar Ogun ga baki ɗaya.”

Taron, wanda shi ne irinsa na farko ya samu halarcin ɗaukacin sarakunan Fulanin dukkan jihohin kudancin Nijeriya.

Ladan Ibrahim Ayawa, Muryar Amurka. Daga Legas, a Nijeriya.



_TTEXT2ALT_
What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.