Tuntube Mu

Mace: Kafin mu ci gaba, ga wata 'yar matashiya.

Namiji 1: Masauraro ku ɗauko alkalami da takarda kusa domin ga wani babban albishir daga sashen Hausa na Muryar Amirka.

Namiji 2: Sashen Hausa na Muryar Amirka ya kirkiro da wata hanya da za ku rinƙa jin muryoyinku kai tsaye, kuna bayyana ra’ayoyinku kullum a cikin shirye-shiryenmu.

Namiji 1: Abinda kawai za ku yi, sai ku kira wannan lamba, watau: biyu, sifili, biyu, biyu, sifili, biyar, tara, tara, huɗu, biyu.

Namiji 2: To malam Ibrahim bari in sake maimaita musu wannan lamba. Watau: biyu, sifili, biyu, biyu, sifili, biyar, tara, tara, huɗu, biyu.

Namiji 1: Idan an kira lambar za a ji wata gaisuwa kamar haka: (waƙa) “VOA, Washington.”

Namiji 2: To, da zarar an ji wannan gaisuwa, sai a matsa ɗaya da biyu a jikin wayar. Sai a ji wannan gaisuwa:

Muryar Wata Mace: A haƙiƙa nan ne Sashen Hausa na Muryar Amirka a birnin Washington DC. Kuma kun faɗa a akwatinmu na barin saƙo a wayar tarho. Ku bada ra’ayi a takaice. Kuma don Allah kada ku manta ku bar suna da cikakken adireshi. (sautin na’ura)

Namiji 1: Ana jin wannan gaisuwa ta Hausa da kuma wannan ƙara (ƙara) sai a fara magana. Duk abinda aka faɗa, na’ura za ta naɗi.

Namiji 2: Za mu sanya mafi ma’ana daga cikin saƙonnin a cikin shirye-shiryenmu na wannan ranar. Mun gode.



What is this? Play Alternate Audio Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.