Tattaunawa domin Kidayar Jama'a

Namiji: To, da farko, su wane ne cikin gidan, kuma shekarunsu nawa?

Mace: To, sunana Fatima Iliya. Ina da shekara ashirin da shidda da haifuwa. Ni mutuniyar ƙasar Nijar ce. Ina zaune a garin Kore, a jihar Damagaram. Ina da miji da kuma yara biyu. Mijina, sunansa Lawali. Yana da shekara arba’in ko arba’in da daya. Dana, sunansa Sa’idu. Yana da shekara 12 da haifuwa. Diyata kuma, sunanta Zara. Tana da shekara 9 da haifuwa.

Namiji: To, wane irin aiki ne kuke yi?

Mace: To, mijina manomi ne da kuma ɗan kasuwa. Muna da gona kusa da gari. A lokacin damina yana shuka hatsi da wake da kuma gurjiya. A ranar Talata yana tafiyan kasuwa. A kasuwa yana saida kaya kamar taliya da filawa. Ni kuma, malamar makaranta ce. Ina aiki a makarantar firamare ta Kore. Ina koyar da harshen Faransanci. Yaranmu suna tafiya makaranta. Ba su aiki.

Namiji: Uwayenki kuma?

Mace: To, ni ‘yar Kore ce. Uwayena suna zauna cikin Kore kusa da gidanmu. Ubana limami ne a babban massalacin gari.

Namiji: Kina da ‘yan’uwa kuma?

Mace: I. Ina da ya da ƙane. Yata tana da shekara talatin da haifuwa. Ta yi aure da wani namiji a Zinder. Tana zaune a Zinder. Tana saida tomatir a kasuwa. Ƙanena yana da shekara ashirin da huɗu da haifuwa. Shi ɗalibi ne a jami’ar ‘Yamai. Yana karatun ilimin kimiyya.

Namiji: To na gode malama.



What is this? Play Alternate Audio Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.