Sarkin noma

Hira da Sarkin Noma

Saude: Ran sarki ya daɗe.
Maidubu: Amin, tare da naki.
Saude: Yaya damina?
Maidubu: Damina, an gode Allah
Saude: To madalla. Allah ya ba da alheri.
Maidubu: Amin, amin.
Saude: To sarki mi kukan noma wannan lokacin?
Maidubu: To mukan noma gero lokacin damina. Akwai kuma gyaɗa da wake da masara. Mata su kan shuka yakuwa da kuɓewa .
Saude: Lalle kuna fama da aiki don samar da cimaka. Lokacin da damina ta wuce mi kuke yi?
Maidubu: To ai akwai noman rani. Ga kaka mukan adana albarkatun gona. Kuma mukan fara shirin noman rani.
Saude: Cikin gonar da kuke shuka gero kuke noman ranin?
Maidubu: A’a akwai lambuna don wannan aiki.
Saude: Mi kukan sa a lambunan naku?
Maidubu: Mukan noma tumatir, tugande, albasa, kabewa, barkono da sauransu.
Saude: Allah ya sa albarka.
Maidubu: Amin, muna bukatar ta sosai.
Saude: To Allah ya ja zamanin sarki, na gode da wannan hira. Mu huta lafiya
Maidubu: Amin, sai an jima.





What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.