Barin saƙo ga tarho.

Muryar barin saƙo ga tarho: Salama alaikum, ana bisa wayar gidan mallam Abdul ne. Babu kowa cikin gida. Don Allah a bar sako kuma za mu maida kiranku. Mun gode. Sai an jima.

Saƙon Amina: Alo, salama alaikum masu gida barka da yau. Barka da ganin wannan lokaci. Ni ce abokiyarku Amina.

Saƙon Amina: Mai gida, malam Abdul ina gajiya? Yaya harkoki? Na ji labarin za ka tafi birnin Accra gobe. Allah ya bada sa’a.

Saƙon Amina: Hajiya Aisha barka da sabuwar shekara. Ina gajiya? Ina gajiyan aikin gida? Ina fatan yaran duka suna lafiya. Ko sun koma makaranta?

Saƙon Amina: Yara barkan ku da sabuwar shekara kuma Allah ya taimake ku wajen karatu. Maryam ina fatan kina taimakon Hajiya wajan kula da kanenki. To Allah ya bada sa’a.

Saƙon Amina: Ni da iyali na, muna lafiya. Mai gidana ya je aiki. Yara suna shirin tafiya makarantar kwana gobe.Ni kuma ina gida. Ina aiki sossai yau saboda shirye shiryen komawar yara makaranta.

Saƙon Amina: Ina kiran ku ne don in gaida ku kuma in gayyace ku zuwa gidanmu gobe da rana. Ina son mu ci abinci gidan mu gobe. Zan dafa abinci mai dadi. Don Allah kada ku kawo abinci saboda akwai kome da kome. Yarana kuma suna son ganin yaranku.

Saƙon Amina: Don Allah ku kira ni yau, ku gaya mini don in san ko kuna iya zuwa.

Saƙon Amina: Na gode kuma sai an jima.



What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.