Rabi: Rakiya ga ɗinkin riga daga Lami. Tana bukatar ta kafin laraba.
Rakiya: Wace irin riga take so?
Rabi: Akwai modal nan tare da atamfarta. Ina da mezir ɗinta nan cikin littafi abokan cinikinmu.
Rakiya: Wannan modal yana da alamar wuya. Ban san yadda ake ɗinka shi ba.
Rabi: Ba laifi; ina gwada miki dalla-dalla yadda ake ɗinka shi. Raba turmin ukku, ki kawo zane ɗaya, da almakashi, da allurai, da kuma alli.
Rakiya: To ga su.
Rabi: Da farko za mu zana yankunan rigar. Yanzu ki ninka zanen biyu, ki daidaita harsunanshi kuma sai ki shinfiɗa shi bisa tebur.
Rakiya: Ya yi haka?
Rabi: I; ya yi. To ga yankunan rigar a zane. Ki bi layukan ki yanka. Ki fara da wuya. Daga nan sai jikin rigar ko gaba, da bayan. Ki tuna muna bukatar ƙyallayen don hannuwa.
Rakiya: Ga yankunan. Wannan rigar ba ta yi mata ƙarama ba kuwa?
Rabi: A’a. Sa zare mai zuwa da launin atamfar ga keken ɗinki. Sa’an nan: da farko ki gama gaban da bayan daidai wuya; ki ɗinke su. Na biyu ki dasa ado ga wuya da bakin kowane hannu. Na ukku ki ɗinka hannuwan ga jikin rigar, bayan haka ki ɗinka rigar ki ɗinka kowane gefe.
Rakiya: To ga su na ɗinka duka.
Rabi: Yanzu kina iya lafi. Ki lafe dukan bakunan rigar. Kuma ki yi haka ga zanen ɗauri da ɗankwalin. Shi ke nan sai ki kakkaɓe su, ki naɗe.
Rakiya: To.