Mai haya: Ana sallama!
Mai gida: Marhaba; shigo.
Mai haya: Barka da yamma Hajiya.
Mai gida: Barka kadai malama, ga kujera, zauna.
Mai haya: To; na gode.
Mai gida: Madalla! Yaya dai? Mi ya kawo ki nan malama?
Mai haya: Ni baƙuwa ce a wannan garin. Ina zuwa nan da zama saboda aikina. Akwai wani gidanki; bayan gidan likita babba; ina son hayar shi ne.
Mai gida: To barka da zuwa garinmu. Gidan yana yi miki?
Mai haya: I, yana kusa da wurin aikina. Ina ganin kamar wadatacce ne, kuma akwai ruwa da wuta. Ɗakuna nawa ne gare shi?
Mai gida: Ɗakunan kwana biyar ne gaba ɗaya, kowane da fanka. Babban gidan yana da ɗakunan kwana huɗu da gidan wanka biyu, da gwadala; kuma waje akwai wata gwadala da ‘yar mangaza. Daura da shi, akwai wani ƙarami mai ɗaki ɗaya da falo.Shi ma da ƙaramin gidan wanka. Kuɗin hayar jikka tamanin ne duk wata.
Mai haya: Ana iya rage kuɗin Hajiya? Akwai biyan wuta da ruwa.
Mai gida: Malama ki duba, ginin na zamani ne; ga mai gadi. Mai gadi yana da bukkarshi. Yana sharar fili da ban ruwan itace kowace rana. Idan kina bukatarshi, kina iya biyan shi jikka biyar ga wata. Hayar kuma saba’in da biyar. Ina karɓar biyan wata ɗaya adibas.
Mai haya: Yaushe nike fara sa kayana?
Mai gida: Yau daidai mutuwar wata ne kuma gida yana shirye. Kina iya shiga gobe. Bari in ba ki mabuɗai. Idan kina bukatar wani abu, ki sanad da ni.
Mai haya: To, na gode.
Mai gida: Madalla. A yi zama lafiya.