Sabon Shirinmu
Masu sauraro albishirinku! Muna gabatar da wani sabon shirin da muke kira Koyarwa a Yau. Cikin wannan shiri za mu duba harkar ilimi a ƙasar Hausa. Za mu yi hira da ma’aikata daga gwamnati da ƙungiyoyi. Za mu yi masu tambayoyi a kan irin nasarori da suke samu da kuma shirye-shiryen da sukan kafa. Za mu kuma tattauna da malaman makaranta a kan irin kalubalen da sukan fuskanci a kowace rana. Haka kuma za mu yi magana da ɗalibai game da karatun da suke yi.
Za mu kewaya duniya mu yi hira da ma’aikata da malamai da ɗalibai daga ƙasashe daban daban. Daga ɗaliban jami’a a Amurka zuwa ‘yan makaranta a wani makarantar firamare a kasar Afghanistan. Muna magana da su don mu gane yadda suke bambanta.
Ku zo ku ji bayyanai da ra’ayoyi a kan halin da aikin bada ilimi ke ciki a ƙasashenmu.
A kowace sati za mu duba wani shirin da wata makaranta ke yi a ƙasar Hausa. Haka kuma za mu nemi ra’ayoyi daga mutane a ƙasar Hausa.
Za mu fara gobe da wata hira da muka yi da farfesa Amadu Lawal na Kano. Ya yi mana bayanai a kan wata sabuwar makarantar firamare da aka buɗe a Kano.
Muna fatan za ku sauraremu kowace ranar Laraba a ƙarfe takwas na marece. Koyarwa a Yau. Sabon shirin na sashen Hausa. Zo ku saurara.
|