Matsalolin Addini a Najeriya

Introduction: Yanzu kuma ga hirar da Nasiru Adamu el-Hikaya ya yi da shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya reshin arewa maso gabas wanda yake aiki da ECWA Bauchi DCC watau Reverend Reverend Shuaibu Byel. Sun zanta ne akan rikicin da ake fama da shi yanzu haka a ƙasar Najeriya da kuma matakin da ƙungiyarsa ta ɗauka cewa Kiristocin Najeriya su kare kansu daga hare-haren da ake kai musu.

Reverend: Eh abinda yake faruwa a cikin Najeriya abin takaici ne, abin ban razana, abin ɓacin zuciya ƙwarai gama abinda yake faruwa a sashin arewa maso gabas, wannan sashi jihohi huɗu yanzu kama daga Maiduguri, Yobe, Gombe, ga shi yanzu Adamawa. Rayuka ana ta kakashe su kawai kamar dabbobi, kuma waɗannan mutane suna fita fili su ce su suka yi. Waɗannan al’amura abubuwa ne na baƙin ciki kuma ya kamata ahhh matakan da shi ka ji a wajen ehh shugaban CAN na ƙasa su ne waɗanda aka gani ya kamata a ɗauke su domin ya zama dole kowane ɗan Adam, ba wai Kirista kawai ba ya zama da cewa yana da bayanin cewa ya san abinda ya shafe shi , ya kuma tsare kada wani abu mai muni ya faru da shi. Ai ba za ka bar garwashin wuta ya faɗa kan cinyanka ka barshi yana ta cinka ba dole ka tura ka yar, ko kuma kana da ruwa sai ka kashe, ruwan.

Reporter Nasiru Adamu: To wannan mai bishare ya nuna kamar yadda shi Bishop Ayo Oritsejafor ya faɗa cewa daga yanzu mabiya za’a basu umurnin su riƙa kare kansu. Ta wane irin yanayi ne zasu na kare kan nasu?

Reverend: Kare kai ina ji ba abu ne sabuwa ba, yana nan cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan da cewa muna da damar abinda ya shafi ‘yancinmu mu kuma tabbatar mun san abinda ‘yancinmu ne mu nemi hakinsa a wajen hukuma. In ta gaza kuma a faɗa mata kamar yadda yanzu ka ji ana faɗa da cewa gwamnoni da sarakunanmu na gargajiya da shugabaninmu na siyasa basu nuna cewa sun nuna damuwa da takaici kan abunda ke faruwa ba don ba matakin da ma suka fara,suka taɓa yi. Muna tsoron kada wani abu ya zama cewa akwai yaƙin basasa a ƙasa nan domin abune mai muni wadda idan za’a ce za’a yi yaƙin basasa, amma gaskiyar kenan shi ne muna da baƙin cikin abinda ke faruwa. Ni mutumin arewa ne, kai mutumen arewa ne,abubuwan da muke yi suna faruwa a wajenmu, ba abubuwan da za su kawo mana ci gaba ba ne a wannan yanki.

Reporter Nasiru: Mai bishara in ka duba yaya kuke ɗaukan wannan al’amari ne a ce wai wani mutun shi guda ɗaya misali ya hida sanarwa ya ce Kiristoci misali su, an ba su ko kwana ukku ko mutanen kudu su koma kudu, bayan kuma ku mabiyannan ma ku ‘yan arewa ne, gidanku ne, iyayenku da kakaninku a nan suke. Yaya kuke ɗaukar wannan labari? Kuna ɗaukansa da wani matsayi mai ƙarfi ? [interruption]

Reverend: Fasarar abinda ya zama muna da damuwa ɗin kenan. Yaya za’a yi ta bada kwanaki wa wasu mutane? Waɗansunmu ba mu ‘yan Najeriya ba ne ba?

Reporter Nasiru: Ba kwa jin in kun ce wannan saƙo na mabiya su kare kai, watakila wasu za su ɗauka cewa kawai su fita da makamai ne su yi ta faɗa da ‘yan uwansu musulmi?

Reverend: Eh to yana yiyuwa, abinda ya faɗa ya ce kowa masani ne idan a cikin Christianity ne. idan an ce ka kare kanka, ya nuna cewa idan ka ga wani abu da danja sai ka sanar da wuri don a taimake ka. Idan ka ga ma cewa ga wasu ana kan cutarsu, ka faɗi Magana da wuri. Jami’an tsaro a kullum sukan faɗa mana da cewa idan mun ji abu ƙis, mu faɗa kuma suna ba mu lambobin wayoyinsu don haka wannan mataki na kariya, sai a yi shi.



_TTEXT2ALT_
What is this? Play Alternate Audio Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.