Matsalolin Halin Zaman Jama'a a Nijeriya

Reporter: Shin me ya sa ne al’amura suke ƙara lalacewa ne a Najeriya idan aka yi la’akari da matsalar matakan tsaro da yawan zaman kashe wando, da dai sauransu, Alhaji Yusuf Maitama Sule Ɗan Masanin Kano, dattijo ne wanda ya ga shekaranjiya da jiya da kuma yau. Ga amsar da ya bayar da aka masa wannan tambayar:



Alhaji Yusuf: Jiya, ana zancen zamanin su Sardauna da su Tafawa Balewa ko? Na taɓa faɗi na ce da za’a ɗauki aƙidar su Sardauna, aƙidar Bafulatanin daji, da dukan abinda ya damemu a Najeriya za mu samu ansa.  Rikici ne na addini, rikici ne na Kabila, rikici ne na siyasa, rikici ne na zamantakewa;  duk aƙidar Sardauna za ta yi maganinsa. Jam’iyyar da muka fara yi a arewa ba ta siyasa ba ce, ita ce NPC,  alif ɗari tara da arba’in da tara a watan June, a Kaduna, muka kafa jam’iyyarnan.  Amma wanene shugaban wannan jam’iyar?  Wanda yake shugaban wannan jam’iyar shine Dr R.B. Dikko Kirista ne. Muka zaɓi kirista a alif ɗari tara da arba’in da tara shekara sittin da ukku ko da biyu da suka wuce, ya zama shugabanmu, da jam’iyar NPC ta zama ta siyaya Sardauna ya kama shugabanci.



Yana Premier ɗin nan, likitansa mai duba shi, Dr Ishaya Audu, Kirista ne, mai kula da sha’anin tsaro, a ofishinsa ko kuma a ƙasar ma baki ɗaya, Sunday Awoniyi kirista ne, Bayarabe, daga Kabba, Wa’yannan Kiristoci kowane daga ƙabila dabam dabam, sune suke tare da Sardauna. Bai tsangwame su ba, bai nuna musu ƙyama ba. Ka ga idan sha’anin addini ne, ya kawo amsa, ka ga Sardauna bai nuna ƙiyaya ba game da wani ko? Sardauna ya yi wannan, ya zauna ya ba kowa hakkinsa, ya yi adalci.



Dangane da tattalin arziki, Sardauna na faɗa mana, yana cewa “ba’a gudu da susar ɗuwawu”. Ya ce duk wani ministansa wanda ya ce yana neman kuɗi ko yana so ya je ya yi cikini, ya bar minister ya je ya yi ciniki zan taimaka masa. Amma ba za ka zo kana mulki kana ciniki ba, ba za ta yiyu ba. Ai ba ga banza ba Allah ya yi wani mai sarauta, wani talaka wani mai saye ya yi wani mai sayarwa, wani malami wani jahili.  Kowa yana buƙata kowa, Allah ya yi wannan tsari saboda duk mu samu zaman lafiya. Sardauna ya yarda da wannan.



Reporter: To Ɗan Masani, dangane da zamantakewa kuma fa?



Alhaji Yusuf: Dangane da Zamantawa, ka je gidan Sardauna ka ga yadda yake zaune da mutane in za’a ci abinci. Da direbansa, da akawunsa, da sakatare, da minista, duk tare za’a zauna a ci abinci, bai ƙyame ka ba.



Alhaji Yusuf: Dangane da siyaya kuma, malam Aminu Kano Allah ya jiƙansa, NEPU ya yi NCNC Alliance, Tarka, UMBC ya yi-Action Group Alliance, Sardauna yana yin NPC, yana premier. Amma duka abinda ya tashi, in dai ya shafi Arewa, Tarka ko malam Aminu Kano za su zo su faɗa wa Sardauna ko su faɗa wa Tafawa Balewa. Malam Aminu Kano idan ya je Kaduna Lacca, in ya gama in ya taso zai dawo gida zai tsaya gidan Sardauna. A gaya wa Sardauna Malam Aminu ya zo, ko yana barci ya fito. Su shiga ɗaki su rufe, yaran Malam Aminu suna gunaguni, ‘yan gidan Sardauna suna Allah tsine. Sardauna da Aminu suna ɗaki suna shawararsu ba wanda ya sani. Tarfa idan ya ji za’a yi wani abu wanda yake ba shikenan ba, wanda zai cuci arewa, sai ya zo ya faɗa wa Sardauna ko ya faɗa wa Tafawa Balewa a siyasance akwai wata rigima.



Ga bambamcin siyasa, ga bambamcin addini, ga bambamcin ƙabila, amma muka ɗauka a ƙasar arewa ita ce ta fi komi muhimmanci, a haɗu a zauna lami lafiya. Kuma babban abinda ya kawo wannan –adalci na Sardauna. Don haka nake cewa, idan da za’a ɗauki aƙidar Sardauna , aƙidar Bafilatanin daji.  Me aƙidar Bafilatanin daji? In ka lura Bafilatani yana gaba, ba baya yake ba yana koro shanu. Yana gaba ne shanun suna biye da shi. In ya tsaya a bakin titi ba zai tsallaka ba sai su tsaya. Kai har ma yakan sa ma wasu shanun suna, in ya kira saniya da sunanta sai ta baro garkenta ta taho wurinsa. Me ya sa suke masa biyaya? Su nai masa biyaya saboda ya sadaukar da ransa saboda su. Duk wani abu da yake na jin daɗi ya bayar nasa saboda su su ji daɗi. A daji yake kwana da shanun.



To wannan biyyaya, in an samu biyyaya da zama lafiya, adalcin shugaba da kuma wannan gudumuwa da shugaba yake yi, da sadauka da duk wani abu nasa saboda mabiyansa su ji daɗi, irin wannan muke so. Zaman da aka yi da kenan, aka samu ci gaba, alhamdulillahi, kuma har yau ake tunawa da sauran mazan jiya ɗin nan ake musu addu’a, Allah ya gafarta musu.





_TTEXT2ALT_
What is this? Play Alternate Audio Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.