Addini da Tsaro

Rahoto na Farko

Zainab Babaji: Malaman addinai a jihar filato sun bukaci al’umma da su haɗa kai ba tare da nuna bambanci ba wajen bankaɗo ɓata-gari da ke hallaka ran al’umma da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai aka samu tashin bam a masalacin da Sheikh Sani Yahaya Jingir ke gudanar da tafsirin azumin Ramadan da ya yi sanadin rasa rayuka da dama da kuma wani bam da aka sanya a Iklisiya ECWA ta Tudun Wada da ke nan Jos wanda da dai da yaddar Allah bai hallaka kowa ba. A cewar shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar IZALA Sheikh Sani Yahaya Jingir, salon da maharan ke bi suna da dama don haka ya yi kira wa jama’a da su yi lura.

Sheikh Sani Yahaya Jingir: To, alhamdulilahi na ƙara godiya wa Allah mai girma da ɗaukaka wanda ya zauna da mu a wannan ƙasar mai albarka ta Nijeriya mai yawan al’umma. Karewar tsaro ya kawo mana matsaloli dayawa ciki na kan gaba sai aka samu cibiyar ci-gaban al’umma aka nema a hana shi ne karatu. Aka samu wata ƙungiya tana kiran kanta Boko Haram saboda kariyawa tsaro. Sun ba mutane ... sun kashe a firamare sun kashe a kasuwa sun kashe a masalaci sun kashe a coci. To, babban magana shi ne mu haɗa hannu gaba ɗaya. Kamar yadda Allah ya ce [ARABIC]. Ku taimake ni a kan aiki nagarta da tsoron Allah kar ku taimaka a junanku a kan aikin laifi da ta’addanci. Haka Alƙur’ani ya faɗa. To sai mu lura duk gaba ɗayanmu, mu bai wa gwamnati haɗin kai, mu ma mu zamanto kowa a gidansa da ɗansa da matarsa da haularsa sekuritin gwamnati ne mai zaman kansa. Suna fito wa mutane a tsari na ba-zata. Mi ne ba-zata? Ka ga mutum kana zaton ɗan alheri ne. Ashe, macuci ne. Ranka ma yake nema. To, don haka kenan sun sanya mu masu ba ida ga kowane irin mutum. Mu ‘yan jihar filato ɗin mu Musulumi da Kiristoci da maza da mata da kabila kaza da kabila kaza wanda ba su ga maciji da. To, wannan shi ne tsarin da muke bi, mu haɗo kanmu ga yanda za a yi a zauna lafiya.

Rahoto na Biyu

IZALA

Hassan Umar Tambuwal: Sheik Khalid Usman Khalid Abukurawi wanda ya jagoranci wa’azin bana a jihar Oyo ya yi wannan kiran a madadin ƙungiyar IZALA ta ƙasa a wajen rufe wa'azin bana a masalacin katako da ke unguwar Bodija a Ibadan.

Sheik Khalid Usman Khalid: Ƙungiyar Jama't Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna ta ce a tunatar da mu, lokacin da muka ɗaga hannunumu za mu dangwala ƙuri’a, duk wanda muka zaɓa tun daga kai shugaban ƙasa har zuwa ƙasa, mun ce ga amanan addininmu mun ba ka. Ga amanan jininmu mun ba ka. Ga amananmu dukiyarmu mun ba ka. Ga amanana lafiyarmu mun ba ka. Ga amanan iliminmu mun ba ka. Duk wata rayuwarmu amana ne a hannunka, kai shugaban ƙasa, kai gwamnan jiha, kai ɗan majalisar tarayya, kai ɗan majalisar dattijai, kai ɗan majalisar jiha. Mun damka musu waɗanan amanoni.

To ƙungiyar Jama't Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna ta ce za mu zama manya-manyan azzalumai idan ba mu ci gaba da taimaka musu da ad’uwa ba. Wajibi ne a kanmu yanzu, umurni daga ƙungiyar Jama't Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna musamman cikin wannan wata mai albarka watan Ramadan. Musammam wannan goma na ƙarshe, mu kaskantar da kanmu fiye da yadda muka yi da. Mu kaskantar da kanmu zuwa ga Allah mu nemi taimakon Allah. Mu roƙi Allah ya taimaki Shugaban ƙasa Buhari da mataimakinshi. Da gwamnoninmu na jihohi, Allah ya ba su ikon sauƙe wannan nauyi da muka ɗora musu cikin aminci. Allah ya dawo da tattalin arzikin Nijeriya ya zama fiye da da, fiye da lokacin Yakubu Gowon. Ya zama fiye da lokacin Sardauna da Tafawa Balewa. Mu ci gaba da roƙon Allah. Shi Allah, ba abinda za ka roƙeshi ya ce ya yi yawa. Shi Allah fushi yake da ke ma in ba ka roƙonshi.

Shugaban ƙungiyar Jama't Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna na ƙasa Sheik Abdulahi Bala Bini Zakariya na Ibelau, ya ce lallai ne yana mana umurni, ba shawara yake ba mu ba. Umurni yake mana. Kafin mu roƙa wa kanmu abu ɗaya, mu roƙa wa shugaban ƙasa Buhari, da gwamnoni da muka zaɓa, mu roƙa musu goma tukuna. Ya ce a matsayinshi na shugaban Sunna, ba wai ya faɗi wanna da son rai ba ne. Ya yi koyi ne da imamu Ahl as-sunnah Imam Ahmad Ɗan Hanbali. Wanda Imamu Ahmad ɗan Hanbali ya ce da Allah zai sanar da shi ya ce ya ba shi addu’a guda ɗaya, wacce in ya yi Allah zai amsa nan take, Imamu Ahmad ɗan Hanbali ya ce to ba kanshi zai yi wannan addu’an ba tunda guda ɗaya ce ba wata. Shugabanci zai yi wa. Domin in shugabanci ya ci nasara, ya ci nasara. In shugabanci ya faɗi, shi ya faɗi.

Saboda haka, yaku ‘yan Nijeriya. Shugaban ƙungiyar Jama't Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna ya ce mu san wannan: In shugaban ƙasa ya ci nasara, dukkanmu mun ci nasara. In shugaban ƙasa ya faɗi, mun faɗi.

Aiki na Shidda

Eliza Baba

Zainab Babaji: Shi ma mataimakin sakataren darika ECWA ta ƙasar Reverend Eliza Baba ya ce a matsayinsu na shugaba na addinai dama ya ce Allah ya ba su su riƙa faɗakar da mabiyansu matakan da za su bi wajen ƙarfafa jama’a ta yadda za su zauna lafiya da juna.

Eliza Baba: Dama ne wanda Ubangiji ya bamu a matsayin shuwagabani mu koma, mu bada ilimi ga ‘yan’uwanmu, ga mabiyanmu. Akwai ‘yan’uwana wa ma son Salla. Zai zama da wuya in ɗauka adda in ce zan saresu. Ka gan, akwai ganewa cewa ni ɗan’uwansu ne. Lokacin bukukuwa ban gan abinda ya ... zai hana ni in gayyaci mai salla ya zo mu yi bikin tare. In Christmas ne ko, shi a lokacin salla ya gayyaceni mu zo mu yi zama lafiya tare, mu yi biki tare, mu mu ji daɗi, mu yi rayuwa tare. Ba abinda ya wuce wannan. Wanda ba ku amince da shi ba. Ka gaya ma hukuma. Wanda ya zo yana kusa da kai a cikin Iklisiya, ba ka yarda da shi ba in ma ya kawo wani abu, ya ajiye. Ka tambaye shi ... in ka ga ya tashi ... ka tambaye shi "Mine ne ka ajiye a nan. Zo ka ɗauka ka tafi." Ya kamata mu ... mu zama masu tsaron kanmu. Mu kuma taimaki su polisawa, su sojojin da Allah ya bamu.



What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.