Tarihin Rayuwa

To, tarihina, shi ne. An haifeni a birnin Zaria, inda na yi makarantar firamare. A lokacin da nike da shekara 12 da haifuwa, babana ya samu aiki a wani masana’anta a Abuja. Saboda haka mun tashi daga Zaria mun koma Abuja da zama.

Da muka koma Abuja, na fara sakandare a makarantar gwamnati da ke unguwar Garki. Na kuma samu takardar kammala sakandare a can. Daga nan sai na samu damar yin karatu a jami’ar New York. Na yi shekara huɗu ina karatu a Amurka, kuma na samu digiri a fannin aikin jarida.

Bayan na samu digirin, sai na koma Kano a nan Nijeriya inda na kama aiki a wani gidan rediyo. Bayan shekara biyu a nan, sai na yi aure. Bayan na yi aure, na bar aiki a gidan rediyon. Mun yi shekara uku haka, sai Allah ya yi wa maigidana rasuwa. Bayan mutuwarsa sai na koma Kaduna inda na kama aiki a wani gidan rediyo daban.

Na yi shekara biyar a can. Sai an gaya mini cewa akwai gurbin aiki a sashen Hausa na gidan rediyon Jamus. Na aika musu takardar neman aiki. Bayan wajen sati biyar sai na samu labarin cewa na samu aikin. Nan da nan na koma garin Bonn a ƙasar Jamus. Bayan na yi shekara uku a nan, sai na yi aure da wani namiji. Bayan ‘yan shekaru kaɗan sai Allah ya sa na haifi ɗa namiji. Kowace shekara muna zuwa Nijeriya don mu ziyarci ‘yan’uwa. Wata rana kuma muna so mu koma Nijeriya da zama.

Aiki Na Shidda

Mijina, mutumin Nijar ne. Yana da digiri a fannin aikin noma daga jami’ar Paris a ƙasar Faransa. Bayan ya samu digirinsa, ya koma ƙasar Amurka da zama. A can ya yi aiki a wani babban kamfanin abinci. Yanzu yana aiki a wata ƙungiya a Jamus. Ƙungiyar tana yin aikin noma a ƙasashen Afirka daban-daban.



What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.