Manyan Gobe

Sanarwa

Ga wata sanrawa. Gidan rediyon Imani na sanar da cewa an kafa sabuwar ƙungiya. Ana kiranta ƙungiyar Manyan Gobe. An kafa wannan ƙungiya tare da haɗin kai daga kamfanoni da ƙungiyoyi daban-daban. Wannan ƙungiya za ta yi ayyuka waɗanda suka shafe makarantu a ƙauyuka. Ƙungiyar za ta fara aiki a wasu ƙauyuka guda ɗari a jihohin Kano da Sakwato. Daga baya kuma za a ƙara garuruwa a jihohi daban-daban na arewacin Nijeriya.

Ayyukan da ƙungiyar za ta yi suna dayawa. Za a bada horo ga malamain makarantu. Za a samar da litattafai ga makarantu. Za a yi gyare-gyare a gidajen makaranta. Haka kuma za a samar da na’urorin zamani ga makarantu. A wasu garuruwa kuma za a gina sabbin gidajen makaranta. Duk waɗannan ayyuka za a yi kyauta. Za mu tabbata da cewa kowane ɗan makaranta ya samu ilimin da ya kamata.

Gidan rediyon Imani za ta taimaka ta hanyar bada sanarwa game da shirye-shiyen ƙungiyar Manyan Gobe. Ƙungiyar UNICEF za ta bada taimakon kuɗi. Haka kuma UNICEF za ta aika wasu masanan harkar ilimi zuwa nan. Masanan za su horas da malaman makaranta. Bayan haka kamfanoni daban-daban za su bada taimakon kuɗi. Hakazalika, muna yin kira ga dukkan masu sauraronmu da ku goyi bayan wannan aiki mai muhimmanci.

Aiki Na Shidda

Idan ana son bada taimakon kudi, sai a je shafin duniyar gizonmu inda za a biya kuɗi ta hanyar intanet. Aikin da wannan ƙungiyan ke yi na da amfani ga yara da matasan ƙasarmu. Mu tuna da cewa ‘yan makaranta sun ne manyan gobe. Saboda haka, ya kamata mu haɗa kanmu.



What is this? Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.