Naƙasassu

Zainab Babaji: Gwamnatin jihar Nasarawa ta gina makarantun horar da naƙasassu sana’o’i da ba su ingantaccen ilimi don su tallafa wa rayuwarsu. Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya shaida mana cewa naƙasassu na da gagaruman gudumawa da za su bayar wajen ci-gaba ƙasa da al’umma in har suka samu ilimi mai inganci.

Umaru Tanko Al-Makura: Ah, halin da muke ciki yanzu, Nasarawa, mun … mu … mu … mun buɗa makarantu guda uku na kulawa da naƙasassu a kowane shiyya na mazaɓan Sana … Sanata. Ah, na Lafiya za ya zamanto ita ce cibiya wanda za a fara ma yaro tun daga elementary har ya kai kusan zuwa university. Ko kai kurma ne, ko kai makaho ne, ko mai jujuta ne, ko wanda Inna ta sha shi ne, ko duk wani abinda kake da shi dai, na naƙasa wanda … ah … yaro ke samun wahala wurin gudanar da … ah … karatunsa a makaranta wanda aka yi shi na mutane marasa naƙasa, to mun kawo inda duk wanda yaronsa na da naƙasa ya kawo mana shi, bai zama yaronsa kuma, ya zamo to yaron gwamnati dai. Don Allah, za mu ba yaron nan ilimi, mu ba shi komai da komai, ba tare da mun ce iyayen ma su biya komai ba, don naƙasa ma kawai da Allah ya sa su ciki, wannan babban jin daɗi ne. To dole mu gwamnati mu ga mu yanda za mu tallafa ma wanda suka naƙasa kamar yanda muke taimaka ma wanda suke da cikakken lafiya.

Zainab Babaji: Gwamnan jihar Nasarawa kenan, Umaru Tanko Al-Makura. Shugaban ƙungiyar makafin Nijeriya reshen jiihar Nasarawa, shugaba Oloshu, ya ce a kwanan nan ya kammala digirinsa na biyu a jami’a. Ya yi imanin cewa bada ilimi wa naƙasassu zai ba su damar dogaro da kansu.

Shugaba Oloshu: Wai ya nuna gwamnatin na jiharmu ta kula da mu. Sa’annan kuma, zai kawo mana zaman kai da kai … ah … saboda … ah … irin wannan takan ba mu ƙarfin gwiwa da cewa za mu iya … za mu shiga yin komai … da … ah … da kanmu da kanmu. Ba tare da taimakon wani ba, za mu iya yi. Illolin bara na dayawa. Ga raini. Ga su hatsururuka. Ubangiji ya ta … ya taimaka na yi makaranta zuwa digiri na biyu. Ah yanzu, babu aiki. Muna sa ido ga Ubangiji da kuma gwamnati da za su taimaka su samu mana aikin yi.

Zainab Babaji: Rahotanni na nuni da cewa akwai naƙasassu fiye da miliyan goma a Nijeriya, wanda mafi yawansu a arewacin Nijeriya suke. Zainab Babaji, Muryar Amurka, daga Lafiya, jihar Nasarawa, Nijeriya.



What is this? Play Alternate Audio Print Page Close Window
Close About
The source is the authentic content from which this lesson was developed. The source can prove extremely useful for learners. You can review authentic materials with total confidence that the materials are at the indicated level. You can easily check your overall comprehension of the materials by simply reading the provided translation. Lastly, you can listen to the authentic audio to check the pronunciation of words or phrases.